Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito ministan sufuri na Japan na tabbatar da mutuwar mutum biyar da ke cikin jirgin tsaron gaɓar teku da ya yi karo da wani jirgin fasinja da ya kama da wuta.
Kafar yaɗa labarai ta NHK ma ta ba da rahoton mutuwar mutanen biyar.
Direban jirgin ya samu tsira sai dai ya ji mummunan rauni.
Ana tunanin jirgin da ke gadin gaɓar tekun yana kai kayan abinci zuwa yankunan da girgizar ƙasa ta shafa lokacin da ya yi taho mu gama da jirgin kamfanin Japan Airlines lokacin da yake sauka kan titin jirgi.
Bayanai sun nuna cewa wani jirgin kamfanin Japan Airlines ya kama da wuta a lokacin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin sama na Haneda da ke Tokyo a ranar Talata.
Wani bidiyo daga kafar yaɗa labarai ta NHK ya nuna yadda hayaƙi ke fitowa daga tagogin jirgin saman da kuma ta ƙasansa.
An kuma ga wutar na ci har a kan titin jirgin.
Kafar yaɗa labaran ta NHK ta ruwaito hukumomi na cewa wataƙila jirgin ya yi karo ne da wani jirgin bayan ya sauka a Haneda.
Akwai fasinjoji a cikin jirgin.
Kafar ta kuma ruwaito cewa jirgin ƙirar JAL 516 ya tashi ne daga Hokkaido.


