Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, ta bayyana a ranar Lahadi cewa, mutane bakwai ne suka mutu, yayin da wasu 100 suka jikkata a hadarurruka 41 da aka samu a yayin bikin Eid-el-Kabir na Sallah a jihar.
Kwamandan sashin, Ahmed Umar, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) a Ota cewa, jami’an hukumar sun ceto mutane 195 da hadarin ya rutsa da su ba tare da sun ji rauni ba a cikin wannan lokaci.
Umar ya ce, jami’an sintiri na musamman na FRSC ne suka gudanar da aikin ceton daga ranar 6 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Yuli.
Kwamandan sashin ya kara da cewa, motoci 71 ne suka hadu da hatsarin guda 41 a lokacin bikin Sallah.
“Yawancin hadarurrukan sun faru ne saboda saba ka’idojin zirga-zirga.
“Masu ababen hawa na bukatar su rika bin ka’idojin zirga-zirga a koda yaushe, domin hana afkuwar hadurran da za a iya kaucewa a kan babbar hanya,” in ji shi.
Umar ya ce, hukumar za ta ci gaba da wayar da kan masu ababen hawa ta hanyar wayar da kan jama’a daban-daban kan tuki lafiya.