fidelitybank

Mutum 68 ne a hannun ƴan bindigar da suka tare jirgin ƙasa

Date:

Akalla mutum 68 rahotanni ke cewa na hannun ‘yan bindiga da suka kai hari jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Wani bidiyo da aka fitar wanda ya rinka yawo har a kafofin sada zumunta, na tabbatar da cewa ‘yan bindigar na rike da mata 41 da maza 22, sai kuma yara biyar.

Wannan na zuwa ne mako biyu bayan kai kazamin harin bam a jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, mutane da dama sun rasa rayukansu baya ga wadanda aka jikkata.

Mako guda bayan harin hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen kasa a Najeriya ta fitar da sanarwar da ke cewa har yanzu akwai fasinjoji 146 da ba a ji duriyarsu ba.

Sai dai shugaban bankin manoma, Mallam Alwan Hassan, da ya samu kubuta a makon da ya gabata shi ya bada alkaluman mutanen da ke hannun ‘yan bindigar a lokacin da ya ke bayyani kan halin da ya tsinci kansa.

Bayan kai harin, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sun san da cewa za a kai harin, sannan ya shaida cewa dama mayakan Boko Haram yanzu na cin karensu babu babbaka a dazukan yankunan Kaduna har zuwa Neja.

nigeria legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji a Neja

Rundunar Sojin Kasa, ta tabbatar da mutuwar wasu daga...

Kungiyoyi 110 suna bukatar mu yi musu rijista – INEC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da samun buƙatu...

Majalisar dokoki na son Iran ta yanke hulɗa da hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya

Majalisar dokokin Iran ta kaɗa ƙuri’a domin yanke hulɗa...

Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kashe-kashen Benue

Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana...

Ba dan mun yi wa Iran barna ba da har yanzu ba ta nemi sulhu ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada cewa harin...

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan masu leken asiri

Kamfanin dillancin labarai na sashen shari'a a Iran ya...

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...
X whatsapp