Akalla mutum tara ne suka mutu sakamakon turmutsitsi a wani filin wasa da ke babban birnin El Salvador, San Salvador.
Lamarin ya faru ne bayan masu sha’awar kallon wasan kwallon kafa sun yi kokarin shiga filin wasan bayan an rufe kofar shiga.
Tuni aka dakatar da wasan da aka shirya bugawa tsakanin ƙungiyoyin Alianza da kuma Fas.