Mutum 13 sun mutu a wani hatsarin jirgi da ya rutsa da su a kan titin Bida zuwa Mokwa a jihar Naija.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutum shida daga ciki mata ne da ke kan hanyarsu ta kai ƙawarsu amarya da ta yi aure.
Rahoton ya ce take suka mutu bayan faruwar haɗarin.
Ƙanin ango na cikin wadanda suka rasa rayukansu.
Wadanda suka shaida faruwar lamarin sun ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙauyen Lukoro da Wuya a kan titin Bida zuwa Mokwa a yammacin Juma’a.
Kwamandan hukumar kale hatsari ta Najeriya a |Naija Kumar Tsukwam wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutum 13 ne suka mutu.
Ya ce haɗarin ya faru ne “tsakanin wata Toyota Corolla da Nissan ta haya da suka yi gaba da gaba, kuma mutum 13 sun mutu,” in ji Tsukwam.