An bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar Filato, Caleb Mutfwang, a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana hakan a ranar Litinin.
Shugaban hukumar ta INEC, Musa Yusuf, bayan tattara kuri’un da jam’iyyu suka samu a zaben, ya ce Mutfwang ne ya samu kuri’u mafi rinjaye inda ya doke dan takarar jam’iyyar All Progressives Nentawe Yilwatda.