Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bayyana wadanda jihar ba za ta kada wa kuri’a a zaben 2023 ba.
Wike ya ce mutanen Rivers ba za su zabi ‘yan takarar da suka ki jinin jihar ba.
Da yake jawabi a taron yakin neman zaben kananan hukumomi na jam’iyyar PDP na jihar a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndoni (ONELGA) a ranar Litinin, ya ce zaben 2023 yaki ne na gamawa.
A cewar Wike: “Hakan ne kuke san wadanda suka tsani jihar Ribas, haka kuke san wadanda suke kaunarmu. Idan kuna ƙin Jihar Ribas, ba za mu ba ku ƙuri’ar mu ba.
“Za mu ba wa masu kaunar jihar Ribas kuri’ar mu ne kawai. Dole ne ku saurari shugabanninku ta hannun DG (darektan janar) na yakin.
“Za su dawo wurinka, su zaunar da kai, su faɗa maka inda za mu dosa. Yaƙi ne don gamawa. Kar a ji tsoro. Za mu yi nasara a ƙarshen rana. Kun san cewa a ko da yaushe munyi nasara. Za mu ci gaba da yin nasara.”