Zababben gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana a matsayin karya, labarin da ake yadawa cewa, ya saba alkawarinsa na kawar da koma bayan albashi da kuma kudaden fansho.
Zababben gwamnan, wanda ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labari, ya bayyana cewa ba zai bar komai ba.
Ya kuma kara da cewa, duk abin da ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe zai cika.
Ademola Adeleke ya fito a wata hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi harkokin mulki a jihar Osun.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa Olawale Rasheed, zababben gwamnan ya bayyana hakan a matsayin karya daga cikin gidan wuta.
Har ila yau, Adeleke ya ci gaba da cewa, a duk tsawon hirar da aka yi da shi, bai taba yin watsi da alkawarin da ya dauka na cire jiga-jigan albashin ma’aikata da ‘yan fansho da alawus-alawus da kuma kyautata rayuwar al’ummar Osun ba.