Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya yi kira ga masu zabe da kada su zabi kabilanci, sai dai su lura da halinsu.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Akure a wajen taron da aka yi na neman goyon bayan al’ummar jihar Ondo a zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Ya bayyana cewa shi da abokin takararsa, Ahmed Datti mutane ne da ake iya gano su, inda ya ce idan aka zabe su a matsayin shugaban kasa, ‘yan Najeriya za su yi alfahari da kasarsu kuma za su samu tsaro.
Obi wanda ya ce shi mai rowa ne amma ba ya cin hanci da rashawa, ya kara da cewa hakan ne ya sa zai iya ceto al’ummar jihar Anambra a matsayinsa na gwamna.
“Sun ce ni mai rowa ne, yanzu muna son masu rowa domin mu rike kudin. Muna so mu tabbatar mun yi amfani da kuɗin ku don sauya ƙasar.
“Kada ku zabi kabila, idan suka ce lokaci ne nasu, ku ce musu lokaci ne na ku don kwato kasar. A shirye muke mu ceto kasar.
“Wannan zaben ya shafi hali ne. Kun san tarihinmu, makarantar da muka je, ba mu san shekarun su ba,” inji shi.