Gwamnatin jihar Borno ta yi gargaɗi ga mazauna birnin Maiduguri da suka fuskanci mummunar ambaliya, game da kiwon lafiyarsu.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labaran jihar ta fitar, ta yi kira ga al’umma su ɗauki matakan kare lafiyarsu da tsaron da muhimmanci fiye da komai.
Ma’aikatar ta zayyana wasu shawarwari da take son jama’a su kula da suka haɗa da:
Kauce wa saye ko sayar da ko kuma cin abincin da ya gurɓarta da ruwa ambaliya. Saboda a cewarta duk bincin da ya gurɓata da ruwan ambaliyar zai iya haifar da hatsari ga lafiya.
Sannan da saye ko sayar da ko cin naman dabbobin da suka mutu (Mushe), ”Kowane irin mushe na ƙunshe da guba”, a cewar ma’aikatar.
Hukumar ta kuma gargaɗi mutane su guji sace ko ɓarnatar da kayan gwamnati ko na wasu mutane.
Daga ƙarshe ta kuma yi kira ga mutane su kauce wa yin ninƙaya ko wanka a ruwan da ke tsaye.”Shi gurɓataccen ruwa koda an tafasa shi, ba za ka raba shi da matsalolin da za su iya yi wa lafiya illa ba”, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.
Ma’aikatar yaɗa labaran ta ce duk wanda aka samu da laifin fatali da waɗannan shawarwari zai fuskanci fushin hukuma.
A farkon makon da muke bankwana da shi ne dai wata mummunar ambaliya da ba ataɓa ganin irinta ba cikin sama da shekara 30, ta auka wa birnin Maiduguri, lamarin da ya shafi kusan mutum miliyan biyu a cewar gwamnan jihar.
Ambaliyar ta kuma yi sandin mutuwar aƙalla mutum 37, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar NEMA ta bayyana.