Gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar Asabar, jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta yi kira ga al’ummar shiyyar Kudu maso Yamma da su kada kuri’a ga ‘yan takarar jam’iyyar.
Musamman jam’iyyar mai mulki ta bukaci mazauna jihohin Ogun, Legas, da Oyo da su marawa ‘yan takarar APC baya.
An yi wannan kiran ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta hannun Hon. Isaac Kekemeke, mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (South-west).
Karanta Wannan: Mu na jan kunnen mutanen mazauan Legas – ‘Yan Sanda
Jigon na jam’iyyar APC ya yabawa ‘yan Najeriya daga dukkan yankuna kan goyon bayan zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kuma bukaci yankin Kudu maso Yamma da su marawa ‘yan takarar jam’iyyar baya a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 11 ga watan Maris.
Kekemeke, tsohon sakataren gwamnatin jihar, SSG, kuma shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO, ya bayyana cewa al’ummar kudu maso yamma za su ci gajiyar shugabancin Tinubu idan suka yi amfani da kuri’unsu wajen kafa gwamnonin APC da ‘yan majalisar jiha a jihohinsu. .
Ya kuma bayyana kwarin guiwa kan iyawa da kuma niyyar shugaban kasa na canza ruwayar da kuma rage wahalhalun da kasar ke fuskanta a halin yanzu sakamakon karancin naira.
Kekemeke, ya kuma yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, da ta samar da daidaito ga dukkan ‘yan takara a lokacin zabe mai zuwa.