Gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Raɗɗa, ya ce kawo yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu kan kiraye-kirayen da suke yi wa jama’ar jiharsa na tashi tsaye wajen kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya ce kawo yanzu akwai garuruwa da dama a jiharsa da ‘yan bindigar basa marmarin shiga, saboda matakan kare kai da mazaunansu suka ɗauka.
Hakan kuma ya ce ba wai suna kira ga al’umma su tashi su ɗauki makami ba ne, sai dai don su kare kansu, saboda jam’an tsaron da ake da su a Najeriya ba za su iya kare ‘yan Najeriya ba saboda sun yi kaɗan.
Dikko Raddan ya ce Abun da muka ce da mutane shi ne su bamu matasansu mu basu horo, mu basu abubuwa da zasu iya bayar da tsaro ga kawunansu, kafin jami’an tsaro su kawo musu dauki” inji shi.