Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga al’ummar jihar su kwantar da hankula, yana mai cewa jami’an tsaro na aiki domin tabbatar da tsaron lafiyar jihar.
Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a ƙaramar fadar sarki da ke Nassarawa, Alhaji Aminu Ado ya ce, mutane su yi addu’ar samun zaman lafiya.
”Jama’a a kwantar da hankula, jami’an tsaro na aiki, domin tabbatar da tsaron lafiya”.
Da asubahin yau ne Alhaji Aminu Ado ya koma Kano, kwana biyu bayan gwamnan jihar ya tuɓe shi.
Shi ma kwamishinan ‘yan sandan jihar cikin wani jawabi da ya yi a shalkwatar ‘yan sanda da ke Bompai ya yi kira ga mazauna birnin su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai.
CP Gumel ya ce, jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.