Wani likita ya shaida wa jaridar Daily Monitor ta Uganda cewa, barasan nan mai guba da ta yi sanadin mutuwar mutum 14 a arewa maso yammacin Uganda, ta makantar da wasu da dama.
Rahotanni sun ce mutanen sun sha barasar ne wadda ake hadawa a gida mai suna Pineapple Flavoured Gin, a karshen makon da ya wuce a lardin Madi-Okollo.
Dr Onesmus Misoa, wanda likita ne a asibitin da aka kai mutanen ya ce wasu daga cikin wadanda suka sha barasar baya ga wadanda suka mutu, sun fara rasa ganinsu, yayin da wasu kuma gaba daya sun makance.
Tuni dai ‘yan sanda suka kama mutum hudu a kan afkuwar lamarin, yayin da mai kamfanin da ake sarrafa barasar kuma ya arce.


