Ma’aikatar lafiyar Gaza da ke karkashin Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe ya karu zuwa 10,569, a cikinsu mutum 4,324 kananan yara ne, tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-haren ramuwar gayya bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.
An dai samu karin mutuwar mutum 241 a Gaza tun bayan wallafa adadi na baya-bayan nan a jiya, Talata.
Shugaba Joe Biden na Amurka a baya ya tuhumi sahihancin alkaluman ma’aikatar lafiyar ta Gaza – sai dai Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce ta yi imani abin amincewa ne.


