Hukumomin Falasɗinu sun ce adadin mutanen da suka mutu a yankin Gaza sun kai fiye da 4,00
Ma’aikatar lafiyar yankin da ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce aƙalla mutum 4,385 ne aka kashe a yankin Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce adadin ya haɗar da ƙananan yara 1,756.