An kuɓutar da gwamman mutane a wani taho mu gama tsakanin jirgin ƙasa da wata motar bas a birin Ikeja da ke jihar Legas.
Hatsarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla uku.
Masu aikin ceto sun samu nasarar fito da wasu mutane 84 daga tarkace a safiyar Alhamis.
Wani jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Ibrahim Farinloye ya ce jirgin ƙasan ya fito ne daga Abeokuta zuwa Legas, inda daga nan ya buge wata motar bas ɗauke da ma’aikatan gwamnatin jihar Legas lokacin da motar ta yi kokarin gutsawa daga layin dogo.
Mutane sun taru lokacin da ake aikin ceto, inda suke kokarin ba da tasu gudummawa