fidelitybank

Mutane sama da 90 sun jikkata tare da mutuwa bayan Tamkar Fetur ta yi bindiga a Jigawa

Date:

Akalla mutane 90 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashewar wata tankar mai a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa a ranar Talata.

Shi’isu Adam, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da NAN a ranar Laraba.

Ya kuma ce an kwantar da wasu mutane 50 a asibiti sakamakon raunukan da suka samu sakamakon fashewar.

“Da misalin karfe 11:30 na daren ranar Talata a garin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, direban tanka ya rasa yadda zai yi a kusa da jami’ar Khadija inda ya fashe.

“Direban ya bar Kano ya nufi Nguru a Yobe lokacin da hatsarin ya afku,” in ji Adam.

Ya ce: “Mun damu cewa duk da gargadin da ‘yan sanda ke yi wa mutane da su kaucewa faruwar hadurran da suka shafi tankunan mai, har yanzu suna aikata irin wadannan abubuwa.

“Mutane sun taru a kusa da wurin da hatsarin ya faru, shi ne dalilin da ya sa aka samu asarar rayuka”.

Kakakin ya ce za a yi jana’izar mutanen da da misalin karfe 9 na safiyar Laraba.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata na samun kulawa a babban asibitin Ringim.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp