Mutane da dama a shafukan sada zumunta na ci gaba da yin Alla-wadai da far wa jami’an zaɓe a jihar Adamawa, ciki har da wani dattijon farfesa wasu suka yi wa jina-jina.
Ana dai ta kira ga hukumomi a kan su gaggauta kama waɗanda ake zargi kan wannan aika-aika, tare da gurfanar da su a kotu.
Farfesa Abdullahi Zuru dai ya kasance tsohon shugaban jami’ar Usman Danfodiyo ta jihar Sokoto, inda ya je aiki jihar Adamawa a matsayin jami’in INEC don cikon zaɓen gwamna da aka yi ranar Asabar.
Ita ma, ƙungiyar tsoffin ɗaliban Usman Danfodiyo ta yi Allah-wadai da cin mutuncin da aka yi wa farfesan.
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta yi kira ga hukumomi su gaggauta kamo waɗanda ake zargin don hukunta su.
A jiya Lahadi ne wani bidiyo ya riƙa nuna Farfesa Abdullahi Zuru, zaune jini ya ɓata sassan jikinsa.
Hukumar zaɓe ta tura shi ne jihar Adamawa a matsayin kwamishina a zaɓen cike giɓi wanda daga bisani ya zo da taƙaddama, lamarin da ya sa INEC ta dakatar da aikin sanar da sakamako.
Far wa Abdullahi Zuru ya zo ne bayan kwamishinan INEC a jihar ta Adamawa Barrister Hudu Ari, ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar duk da cewar ba a kammala tattara sakamakon ba a lokacin


