Kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi ikirarin cewa mutane na son dan wasan gaba Eriling Haaland ya gaza.
Guardiola ya fadi haka ne yayin da yake wasa da dariya cewa ya damu da yanayin Haaland bayan dan wasan Norway ya zura kwallaye biyu a wasan da Man City ta doke Young Boys da ci 3-1 ranar Laraba.
Yayin da Haaland ya sami damar kawo karshen fari na cin kwallaye biyar a gasar zakarun Turai, tsohon dan wasan Borussia Dortmund bayan ya xaura ƙwallo biyu a Young Boys, inda ya haifar da damammaki masu kyau na zura kwallo a duk lokacin wasan.
Duk da cewa Haaland ya zura kwallaye 11 a wasanni 14 a kakar wasa ta bana, wasu na ganin kwazonsa a kungiyar Guardiola bai yi daidai da na kakar wasan data gabata ba inda ya zura kwallaye 52 a tarihi.
Da aka tambaye shi ko Haaland ‘ya damu’ game da rashin samun ƙarin dama, Guardiola ya gaya wa TNT Sports bayan nasarar da Man City ta yi akan Young Boys: “Yawa, da yawa. Gaskiya, na damu sosai!
“Mutane suna tsammanin zai ci kwallaye hudu a kowane lokaci. Jama’a suna son ya gaza. Na yi hakuri amma wannan mutumin zai zira kwallaye a duk rayuwarsa, tare da yiwuwar ya zama babban barazana. “


