Sabbin bayanan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa fiye da mutum miliyan hudu ne suka tsere daga Ukraine domin guge wa yakin kasar kawo yanzu.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan kasar Ukraine 4,019,287 ne suka tsallaka iyaka tun ranar 24 ga watan Fabrairu lokacin da aka soma yakin.
‘Yan kasar Ukraine fiye da miliyan 2.3 a halin yanzu suke Poland.