fidelitybank

Mutane miliyan 25 za su fuskanci yunwa a Najeriya

Date:

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 25 na cikin barazanar faɗawa halin yunwa tsakanin watan Yuni da kuma Agustan 2023 muddin ba a dauki matakin gaggawa ba.

Rahoton wanda kungiyar Cadre Harmonisé ta fitar, wadda kungiya ce ta Majalisar Dinkin Duniya da ke taimakawa wajen samar da abinci mai gina jiki, ya nuna cewa ƙasar na ci gaba da fama da rikice-rikice da sauyin yanayi da kuma hauhawar farashin kayan abinci.

A cewar wata sanarwa ta haɗin gwiwa da hukumar noma da samar da abinci da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya da hukumar bayar da agaji suka fitar, ta ce hakan ya nuna ƙaruwa a cikin mutane miliyan 17 da ke fama da matsalar ƙarancin abinci a yanzu.

Sanarwar ta kuma lura cewa ayyukan ‘yan ta-da-ƙayar-baya ya shafi aikin samar da abinci a yankin arewa maso gabas a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe da kuma matsalar ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Neja.

Sanarwar ta ce Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta ruwaito cewa matsalar ambaliyar ruwa da aka samu a shekarar 2022, ya lalata kadada 676,000 na gonaki wanda kuma ya kawo raguwa a abin da mutane suka girba da janyo ƙaruwar barazanar matsalar ƙarancin abinci ga iyalai a faɗin kasa. In ji BBC.

latest news in nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp