Jam’iyyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, New Nigerian Peoples Party (NNPP), ta yi ikirarin cewa, ta yi wa mambobi miliyan biyu rijista a jihar Borno.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Mohammed Mustafa ne ya yi wannan ikirarin a Maiduguri ranar Lahadi, inda ya yi alfahari da cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin zaben 2023.
Naija News ta fahimci cewa, yawan al’ummar jihar Borno ya kai kimanin miliyan 5.86 a shekarar 2016. Duk da cewa jihar ta yi asarar rayuka sakamakon hare-haren ‘yan tada kayar baya a ‘yan shekarun nan, amma watakila adadin mutanen bai ragu ba saboda sabbin haihuwa.
Da yake magana game da shirin NNPP na sauke jam’iyyar APC mai mulki a zabe mai zuwa, Mustafa ya ce, jam’iyyar tana da farin jini sosai a Borno kuma yanzu ta shirya lashe zaben shugaban kasa ga dan takararta, Kwankwaso.
Ya yi alfahari da samun nasara a matakin jiha, yana mai cewa jam’iyyar na da kwararun dan takarar gwamna da zai iya lashe zabe.