Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Lahadi.
Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasar tare da haɗin gwiwar hukumomin jihar suka bazama domin ceto waɗanda suka ɓacen.
Waɗanda lamarin ya shafa yawanci ƴan kasuwa ne da suke hanyar tafiya zuwa babbar kasuwar Goronyo da ke ci duk ranar Lahadi a lokacin da kwale-kwalen ya kife ɗauke da matafiya kusan 50, amma hukumomi sun ce an samu nasarar ceto mutum 10.
A mako uku da suka gabata ne aƙalla mutum 13 suka rasu bayan wani kwale-kwale ɗauke da mutum 100 ya kife a jihar Neja.
Haka kuma manoma 16 sun rasu wani haɗarin a watan Agustan 2024 a jihar ta Sokoto, sannan a ranar 29 ga watan Yuli, ƴanmata shida sun nutse bayan kwale-kwale ya kife da su a jihar Jigawa.
Ko a kwana biyun da suka gabata, wasu mutum 13 sun mutu a haɗarin kwale-kwale a jihar Neja.