Gwamnatin Sifaniya ta ce har kawo yanzu ba a gano gwamman mutane ba bayan ambaliyar ruwan da ta afku a cikin makonnan.
Kusan mutum 160 ne suka rasa ransu a ambaliyar.
Wani minista a ƙasar Angel Victor Torres, ya ce zai yi wuya a gane irin ɓarnar da ambaliyar ta haddasa yanzu.
Wakilin BBC a Valencia ya ce akwai tashin hankali sosai a kan wannan iftila’i da ya faru.
Akwai wasu wuraren da ba za a iya kai wa gare su ba ma a yayin da masu aikin ceto ke ƙoƙarin kwashe motoci da ɓuraguzan ginin da suka cika titunan yankin.
Wani jami’in hukumar agaji ta Red Cross ya bayyana cewa a yanzu haka muna ɗaya daga cikin wuraren fakewa da aka samar a birnin Valencia, a wannan wajen kaɗai akwai mutum fiye da 600.
Firaiministan ƙasar Pedro Sanchez, ya buƙaci mutane da su zauna a gida sannan kuma su kiyaye da shawarwarin da jami’an ceto ke basu.


