Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane hudu a wani hatsarin mota.
Hatsarin ya afku ne a ranar Alhamis 29/9/2022, da karfe 1110 na kan hanyar Bauchi zuwa Kano, Tashan Mai-Alewa, kuma an ruwaito shi da karfe 1130.
Rahoton ya ce adadin mutanen da lamarin ya shafa sun kai 11, dukkansu maza, daga cikinsu akwai manya bakwai da suka jikkata, yayin da maza hudu suka mutu.
An bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wasu motoci guda biyu, wata mota kirar Vibe Pontiac mai zaman kanta mai lamba BUU457SY, da wata karamar mota kirar Ford Galaxy mini bas mai lamba MSA59XB.
Motar Vibe Pontiac wani Dr. Yahaya Usman Muhammadu ne ya tuka motar.
Hukumar ta FRSC ta ce dalilin da ya sa hatsarin ya faru shi ne karya kayyade saurin gudu da kuma rashin tsaro a daidai lokacin da aka shimfida hanyar.
An kai wadanda harin ya rutsa da su babban asibitin Ningi domin jinyar wadanda suka jikkata cikin gaggawa da kuma tabbatar da wadanda suka mutu kamar yadda rahotanni suka bayyana.