Wani hatsarin mota daya tilo da ya rutsa da wata motar bas Mazda a Oniworo, unguwar Foursquare Camp dake kan titin Legas zuwa Ibadan, ya yi sanadin mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 16.
Ahmed Umar, Kwamandan hukumar FRSC reshen Ogun wanda ya tabbatar da afkuwar hatsarin a Abeokuta, ya ce, hatsarin ya afku ne da karfe 7:50 na safe, inda ya kara da cewa, direban bas din ya yi ta gudu fiye da kima kafin daga bisani ya yi kaca-kaca da tsakar dare. Motar bas ɗin ta yi zafi kuma ta kama da wuta.
“Mutane 20 ne lamarin ya rutsa da su, hudu sun kone kurmus, yayin da mace daya da maza 15 suka samu raunuka


