fidelitybank

Mutane fiye da dubu aka kashe a Najeriya a watan Oktoba – Rahoto

Date:

Wani rahoton da kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a shiyyar Afirka ta yamma ya fitar, ya nuna cewa fiye da mutum dubu aka kashe a Najeriya a watan Oktoban 2023 sanadiyyar hare-haren `yan bindiga da mayakan Boko Haram.

Kazalika rahoton ya ce fiye da mutum 500 ne aka sace don karbar kudin fansa.

Rahoton da bayyana cewa lamarin tsaro ya kara tabarbarewar a Najeriya, daga watan Satumban wannan shekarar zuwa watan Oktoban da ya wuce.

Kamfanin Beacon Consulting, a rahoton nasa na watan Oktoban da ya wuce ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale ta fannin tsaro a sassan kasar da dama.

Ya ce ana fama da matsalar harin `yan bindiga da wasu kungiyoyi, ciki hár da kungiyar Boko Haram da ta IPOB, wato masu fafutukar ballewa da nufin kafa kasar Biafra.

Kuma alkaluman da kamfanin ya fitar sun nuna an rasa rayukan jama`a, an kuma sace mutane a hare-haren da aka kai kan al`umma a kananan hukumomi 266 da ke fadin Najeriya.

Alƙaluman sun nuna lamarin ya fi kamari ne a arewacin Najeriya, inda aka kashe mutum 326 a jihar Borno, jihar Zamfara kuma an kashe mutum 262, Yobe kuma mutum 60, sai kuma Binuwai 38. Yayin da mutum 39 suka rasu a jihar Rivers, Anambara 27, Lagos kuma 19.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp