Kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi al’ummar yankuna su Zamfara da kewaye, Bello Turji, ya ce, asalinsa makiyayi ne kuma mutane suna mamakin yadda ya zama dan ta’adda mai garkuwa da mutane.
Turji, wanda dan asalin garin Fakai a karamar Shinkafi na jihar Zamfara ne, ya bayyana cewa, wadanda suka san shi sun yi mamakin yadda ya fara sata da kashe-kashe.
A wata hirar da ya yi da tashar Trust TV, Turji ya ce: “A baya ni makiyayi ne. Idan mahaifi na na son sayar da Shanunsa, ni ke kai masa kasuwa. Idan na sayar sai in tafi fadar Sarkin Shinkafi kafin in koma gida, kuma sarkin Shinkafi ya san ni. Idan a ka fada masa Turji zai zama dan bindiga, ba zai yarda ba, saboda ya san mu Fulani ba zamu zama barayin Shanu ba. Amma abubuwan da ake mana ya fara yawa.”
Turji ya kara da cewa, a rana guda aka kashe masa ‘yan uwa shida, bayan sacewa iyayensa Shanu sama da dubu. A cewarsa, sun je duk kotunan duniyan nan, amma Shanunsu basu dawo ba.
“An kwashe mana sama da Shanu 1000. A ranar, an kashe ‘yan uwana shida. Iyayenmu sun je kotu, amma a dawo musu da Shanunsu ba. Hakazalika an hada kai da ‘yan sa kai wajen kashe babban yayana. Ina talaka zai samu adalci?” in ji Turji.