Hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC reshen jihar Jigawa, ta ce mutane biyu sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Birnin Kudu/Kano.
Kakakin rundunar, Mista Yahaya Ibrahim, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse.
A cewarsa, hatsarin ya afku ne da misalin karfe 2:50 na rana sakamakon gudu da kuma fashewar taya.
Ya bayyana cewa hatsarin ya hada da wata mota kirar Golf ta Wolkswagen dauke da fasinjoji 11 inda biyu daga cikinsu suka rasa rayukansu sannan wasu tara suka samu raunuka daban-daban.
Kakakin ya ce jami’an hukumar FRSC da suka amsa hadarin cikin mintuna bakwai bayan samun bayanan, tuni suka kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke FMC a Birnin Kudu.


