fidelitybank

Mutane biyu sun mutu a wani sabon hari da aka kai Taraba

Date:

An sake tabbatar da mutuwar mutane biyu a wasu hare-haren da aka kai a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya faru a ranar Juma’a, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), Abdullahi Usman, ya ce a farkon lamarin, ‘yan bindiga sun kai hari a wani gida, inda suka yi amfani da adduna suka farfasa tagar gidan.

A cewarsa, an harbe wata budurwa da ke karatun jarabawa a dakinta.

“Tana karatu a dakinta sai suka bude mata wuta, suka buge ta a baya. Harsashin ya fita ne ta cikinta,” Usman ya bayyana.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun umurci mazauna gidan da su fito waje amma ba su yi awon gaba da kowa ba balle su dauki wani abu mai daraja.

Lamarin na biyu a cewar rundunar ‘yan sandan ya faru ne a unguwar Jerbanbur da ke Jalingo, inda aka kai wa wani malamin addini hari.

Usman ya ce maharan sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi inda suka tafi ba tare da sun yi awon gaba da kowa ba.

Ya kara da cewa, “An garzaya da wadanda suka mutun zuwa asibiti amma sun mutu a lokacin da suke karbar magani.”

Rundunar ta bayyana hare-haren a matsayin wanda ba a saba gani ba, inda ta ce maharan ba sa bin tsarin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Rundunar ‘yan sandan, kamar yadda ya bayyana, ta kaddamar da kwakkwaran bincike domin ganowa tare da cafke wadanda ke da hannu a kisan.

latest legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp