Rahotanni sun ce mutane biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya rutsa da wani jirgin ruwan kasuwanci da ya taso daga Ipakodo, a Ikorodu zuwa Victoria Island, Legas a safiyar Laraba.
An yi sa’a, an ceto wasu 15, yayin da wasu mutane uku suka bace kamar yadda aka yi bayani a kai.
An ce jirgin na dauke da fasinjoji kusan 20 ne a lokacin da lamarin ya faru wanda shaidun gani da ido suka ce ya faru ne da misalin karfe 4:30 na safiyar Laraba.
Shaidu sun yi zargin cewa wadanda suka fara isa wurin ‘yan kamun kifi ne kafin isowar masu aikin ceto daga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da kuma na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA).