Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, kusan mutane biliyan daya a duk duniya suna fama da wani nau’i na tabin hankali, kamar yadda sabbin bayanai na Majalisar Dinkin Duniya suka nuna.
Bayanan da aka fitar a ranar Juma’a sun ce adadin ya fi damuwa, saboda ya hada da kusan daya cikin matasa bakwai. A cewar Tribune.
“A cikin shekarar farko ta cutar ta COVID-19, yawan yanayi na yau da kullun kamar baƙin ciki da damuwa ya haura sama da kashi 25 cikin ɗari,” in ji shi.
Ta ce a cikin nazari mafi girma na lafiyar kwakwalwa, tun farkon karni cewa, WHO ta bukaci karin kasashe da su shawo kan matsalolin da ke kara tabarbarewa.
Bisa ga bayanan, rashin daidaiton zamantakewa da tattalin arziki, matsalolin lafiyar jama’a, yaki, da rikicin yanayi na cikin duniya, barazanar tsarin ga lafiyar kwakwalwa.
Hukumar ta ce, bakin ciki da damuwa sun haura sama da kashi 25 cikin 100 a farkon shekarar cutar kawai.