Wasu iyali mutum bakwai (7) a kauyen Runjin Barmo da ke gundumar Kajiji a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto, sun mutu bayan sun ci rogo.
Iyalin sun mutu jim kadan bayan cin abincin rogo maras kyau wanda ake zargin ya gurbata a lokacin.
Kwamishinan lafiya na jihar, Asabe Balarabe, wanda ta jagoranci wata tawaga mai karfi zuwa kauyen domin jajantawa, ta shaida wa hakimin kauyen Malam Muhammadu Modi Magajin Runjin Barmo cewa wadanda abin ya shafa sun ci rogon ne a lokacin da suke cin abincin dare.
A cewar, Hakimin wadanda abin ya shafa sun hada da mahaifin, Malam Abubakar, matarsa, A’ishatu Abubakar da ‘ya’yansu 5.
Ya bayyana cewa, rogon da ake zargin gidaje kusan 4 ne suka yi amfani da su a kauyen kuma ba a samu labarin wata cuta ba a gidajen.
Magaji a madadin al’ummar yankin, ya godewa gwamnan jihar, Dr Ahmed Aliyu bisa nuna damuwarsa gare su ta hannun Kwamishinan.
Balarabe, yayin da take magana, ta bayyana cewa sun je kauyen ne domin tantance musabbabin faruwar lamarin domin ci gaba da tuntubar gwamnatin jihar domin daukar matakin da ya dace.
Ta ce ma’aikatar za ta dauki samfura daga wani matashi da ke raye bayan cin abincin rogo da ake zargin.
Ta jajanta wa al’ummar yankin da faruwar lamarin tare da addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasa rayukansu.
Ta yi kira ga al’ummar jihar da su tabbatar da gaggauta kai rahoton duk wata bakuwar cuta a yankunansu domin shiga tsakani na ma’aikatar.
A nasa jawabin daraktan lafiya na karamar hukumar Shagari Sani Bello Tambuwal ya godewa kwamishinan bisa damuwar ta da kuma fatan an dore da wannan kokari.