Mutane 9 ne suka kone kurmus a ranar Juma’a, a wani hatsarin mota da ya afku a gadar Omotosho Step Down, kan titin Ore-Lagos a karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) na rundunar Ore, Sikiru Alonge, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya ce hadarin da ya faru da sanyin safiyar yau ya hada da motoci biyu, wata farar motar Toyota Hiace mai lamba FKJ 095 XE da kuma Honda Accord. Motar Saloon, wacce ba za a iya tantance lambar rajista ba.
“Mutane tara ne suka kone kurmus a wani mummunan hatsarin da ya afku a hanyar Ore-Lagos da sanyin safiyar yau. Hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar taya, wanda ya yi sanadiyar yin karo da juna, wanda daga baya ya yi sanadin tashin gobara, wadda ta kone dukkan mutanen da ke cikin motocin da ba a iya gane su ba.” Inji shi.
Alonge ya ce an ajiye gawarwakin wadanda abin ya shafa a dakin ajiye gawa na babban asibitin Ore.
Ya shawarci masu ababen hawa da su rika kiyaye kayyakin gudu, su maida hankali, su yi hakuri, su kuma bi duk ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa yayin tuki domin ceton rayuka da dukiyoyi.