Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta tara biliyoyin Naira gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da wasu masu neman mukamai daban-daban a zaben 2023 suka fitar da miliyoyin Naira don siyan fam din takarar jam’iyyar, inji rahoton Naija News Hausa.
APC ta sanar a ranar Talata mai zuwa a matsayin wa’adin sayen fom yayin da ta ke shirin tunkarar zaben fidda gwani.
Dangane da haka, akalla ’yan takarar gwamna 95 ne suka biya tare da karbar fom din tsayawa takara kafin yammacin ranar Alhamis.
A baya dai APC ta karbi kudi kimanin Naira biliyan 1.630 daga hannun ‘yan takarar shugaban kasa 17, ciki har da mace daya mai neman shugabancin kasar, wadanda suka karbi fom dinsu.
Naija News Hausa ta fahimci cewa, yayin da mazaje masu neman tsayawa takarar su biya Naira miliyan 100 kowannensu, an kuma umurci mace da ta biya Naira miliyan 30 kacal.
Domin kara wadatar da kudin jam’iyyar, jam’iyyar ta karbi kudi daga mutane 241 masu neman kujerun Sanata.
Haka kuma, kawo yanzu mutane 821 ne suka sayi fom din takarar majalisar wakilai.
Idan dai za a iya tunawa a ranar Alhamis din nan, jimillar ‘yan takara 1,505 da ke neman tikitin jam’iyyar a Majalisar Dokokin Jihohi 36 su ma sun biya tare da karbar fom dinsu.
Sakataren kungiyar APC na kasa, Sulaiman Arugugu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar jiya.