Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ba da tabbacin mutuwar mutum 81 sakamakon harin kuskure da wani jirgin sojin Najeriya ya kai kan farar hula a Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya.
Manjo Janar Edward Buba, Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron ne ya bayyana haka inda ya ce mutum 70 ne suka jikkata sakamakon harin.
A baya dai, hukumar ba da agajin gaggawa ta ba da rahoton cewa sama da mutum 85 ne suka mutu sakamakon harin da aka kai, yayin da wasu ƙungiyoyi ke cewa adadin mutanen da suka mutu ya zarce haka.
Hedikwatar tsaron ta kuma ce daga yanzu, za ta tabbatar da inda za ta kai hari ɗari-ɗari kafin jefa bom.
“Za mu ci gaba da aiwatar da ayyukanmu bisa ƙa’idojin aiki wanda hakan muke yi,”
“Game da abin da ya faru a Kaduna, sojoji sun ɗauki darasi kuma za su ci gaba da aiki da shi. Za mu tabbatar ba a sake ganin irin haka ba a gaba.”
Janar Buba ya kuma mayar da martani game da zarge-zargen da wata ƙungiyar arewa ta yi cewa an kai harin ne domin rage yawan al’ummar arewa inda ya ce “rundunar sojin Najeriya ta ƙunshi ma’aikata daga kowace ƙabila a Najeriya. Ko ma me ƙungiyar ta ce, harin ya faru ne a kan kuskure.”