Ƙungiyar ƙwararrun likitocin zuciya da jijiyoyin jini ta Najeriya (ACTSON) ta ce, ‘yan ƙasa fiye da 80,000 ne ke buƙatar tiyatar zuciya kowacce shekara.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Uvie Onakpoya ne ya bayyana haka a Abuja baban birnin ƙasar, lokacin taron ƙungiyar na shekara-shekara.
Ya ce cutukan da ke da alaƙa da zuciya da jijiyoyin jini ne kan gaba wajen haddasa yawan mace-mace fiye da kowacce cuta a duniya.
Dakta Onakpoya ya ce takwas cikin duk yara 100 da aka haifa, na ɗauke da cutukan da suka shafi zuciya.
Ya ƙara da cewa a Najeriya fiye da yara 55,000 ake haifa da cutar zuciya duk shekara.
Shugaban ƙungiyar likitocin zuciyar ya ce a bara, mutum 212 ne kaɗai aka yi wa tiyatar zuciya, saboda tsadar tiyatar da sauran matsaloli.
Dakta Onakpoya ya ce ƙungiyar ta sha kira ga hukumomin Najeriya a kan su kafa dokar da za ta sauƙaƙa yin tiyatar zuciya.
A cewarsa, ta yadda masu jinyar za su samu sauƙi wajen zuwa asibitocin gwamnati da masu zaman kansu don yi musu tiyatar.