Kusan mutum 80,000 ne za su rubuta jarrabawar JAMB da aka sake tsara rubutawa ranar 6 ga watan Mayu.
A cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar Fabian Benjamin ya fitar, ya ce an samu jinkirin ne sakamakon aikin tantance sakamakon jarrabawar da aka rubuta.
Sanarwar ta ce ɗaliban da aka tantance a cibiyoyin rubuta jarrabawar, amma ba su rubuta jarrabawar ba, da waɗanda ba a tantance bayanansu ba, da waɗanda aka samu saɓanin bayanansa za su samu saƙonnin rubuta jarrabawar.
Sanarwar ta ce “Waɗanda suka samu matsaloli a lokacin rubuta jarrabawarsu, ba za su ga sakamakonsu ba, a maimakon haka za su samu saƙon sake rubuta jarrabawar.
Hukumar ta ce sakamakon zaman gaggawa da ta yi ranar 30 ga watan Afrilu, ta saka ranar 6 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a sake rubuta jarrabawar ga waɗanda ba su rubuta jarrabarwa ba.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ɗaliban da abin ya shafa su fitar da takardun bayanansu na jarrabawar tsakanin 4 zuwa 5 ga watan Mayu, domin sanin lokaci da kuma wurin da za su rubuta jarrabawar.