Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ba da rahoton kisan mutum takwas a fashewar rumbun mai a Conakry, babban birnin Guinea.
AFP ya ambato wani jami’i a asibiti na cewa “an kawo mutum takwas da suka ƙone zuwa asibitin Ignace Deen,”
Tun farko kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wani jami’in ɗan sanda ya ce mutum takwas sun mutu.