Wasu matafiya 8 ne suka mutu a ranar Laraba, yayin da wasu 47 suka jikkata a wani hatsarin da wasu manyan motoci biyu suka yi a hanyar Potiskum zuwa Nangere a jihar Yobe.
Hadarin ya afku ne a lokacin da matafiya ke kan hanyarsu ta zuwa wata shahararriyar kasuwar shanu ta mako-mako a garin Potiskum, inda daya daga cikin motocin ya rasa yadda zai yi, ya kuma yi karo da daya.
Wani ganau mai suna Adamu Hassan ya shaida wa manema labarai cewa an kwashe gawarwakin zuwa asibitin kwararru na Potiskum, yayin da wadanda suka jikkata kuma aka kai su babban asibitin Sabon Garin Nangere domin kula da lafiyarsu.
Muhammad Kawuwale, ma’aikacin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an tabbatar da mutuwar mutane takwas, yayin da 47 suka samu raunuka daban-daban.
“Mun kuma tattara cewa 47 sun samu raunuka. A cikin wannan adadin, 26 sun fito ne daga Nangere yayin da 21 daga karamar hukumar Potiskum,” in ji shi.
Ya kara da cewa SEMA ta samar da magunguna kyauta da sauran abubuwan da suka dace ga wadanda abin ya shafa.


