fidelitybank

Mutane 8 sun ƙone ƙurmus sakamakon fashewar tamkar mai a Ondo

Date:

Kimanin mutum takwas ne aka tabbatar sun mutu, sakamakon fashewar wata tankar dakon mai a jihar Ondo.

Lamarin ya ƙazance ne yayin da wuta ta kama a daidai lokacin da mazauna garin ke diban mai daga tankar da ta yi hatsarin a daren ranar Lahadi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta ce motar dakon man ta faɗi ne a kan titi, inda kusan dukkanin abubuwan da ke cikinta ya malale. Bayan haka ne mazauna yankin suka mamaye wurin domin dibar man.

“Motar tankar ta fashe inda ta kashe mutum takwas, ta kuma raunata wasu da dama wadanda aka garzaya da su asibiti, kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya shaida wa BBC.

Mazauna yankin da shaidun gani da ido sun ce tankar ta fashe ne a wata unguwa da ke kusa da gidan mai, da kuma wani ginin coci amma babu ko daya da gobarar ta shafa.

Najeriya dai na fuskantar karin kusan kashi 400 na farashin man fetur tun watan Yuni bayan cire tallafin man da shugaba Bola Tinubu ya yi, matakin da ya ƙara iza wutar tsadar rayuwa da tsadar kayan masarufi.

Ƙasar wadda ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka tana shigo da sama da kashi 90 cikin 100 na man da take bukata saboda gaza tace danyen mai a cikin gida saboda lalacewar matatun mai mallakin gwamnati

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp