Kimanin mutum bakwai aka ba da rahoton an kashe a birnin Izeh na ƙasar Iran a wani hari da ƴan bindiga suka kai ranar Laraba yayin da ake zanga-zangar kin jinin gwamnati.
Daga cikin waɗanda aka halaka akwai wasu maza uku – ɗaya shekararsa 10, sauran biyun kuma ƴan shekara 13 ne.
Hukumomin Iran sun bayyana harin a matsayin na ta’addanci yayin da masu zanga-zangar ke zargin sojojin gwamnati da hannu.
Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Isra’ila da hukumomin leƙen asiri na ƙasashen Yamma da ƙoƙarin raba kan Iran tare da neman haifar da yaƙin basasa.