Akwalla mutum 65 ne suka jikkata yayin da wasu jiragen kasa biyu suka yi taho mu gama da juma a kudancin Tunis babban birnin Tunisia.
Babu rahoton mutuwa ko guda sai dai tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti, kamar yadda tawagar masu ba da agajin gaggawa suka bayyana.
“An garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti amma babu wanda ya mutu zuwa yanzu,” in ji kamfanin dillancin labarai na AFP.
Daya daga cikin jiragen na dauke da fasinjoji dayan kima babu kowa ciki, in ji Moez Triaa kakakin hukumar tsaro ta Civil Defence.