fidelitybank

Mutane 61 sun kamu da cutar ƙyandar Biri a Najeriya

Date:

An tabbatar da mutum 67 ne suka kamu da cutar kyandar biri daga cikin mutum 1,031 da aka yi fargabar sun kamu da cutar a jihohi 23, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta wallafa a ranar 11 ga Satumba.

Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC ta ce jihar Akwa-Ibom da Enugu kowacce na da mutum takwas da suka kamu, sai Bayelsa da ke da shida, sai kuma Cross-River mai biyar, da kuma sauran mutum 40 ɗin da suka watsu a sauran jihohi 19.

Darakta Janar na NCDC, Jide Idris ya ce hukumar ta ƙara zage damtse domin yaƙi da yaɗuwar cutar.

“Muna aiki tare da hukumomin tashashin jiragen ruwa domin kiyaye yiwuwar shigo mana da nau’in Clade I na cutar,” inji Idris, inda ya ƙara da cewa suma hukumomin na tashashin jiragen ruwa suna tattaunawa da jihohin da suke bakin boda.

Ya kuma ce suna ƙara inganta ɗakunan gwaje-gwajensu a faɗin ƙasar domin tabbatar da cewa ba sai an yi ta yin jigila ba domin gwajin cutar.

Zuwa yanzu dai ƙasashe 13 ne suka fama da cutar kyandar biri a Afirka bayan ƙasar Guinea ta sanar da mutum na farko da ya kamu.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp