Mutane shida ne su ka rasa rayukansu a Wani haɗarin mota da ya rutsa da su a a garin Tingan Maje da ke Babban Birnin Nijeriya, Abuja.
Haka kuma mutane 9 sun ji raunuka a haɗarin da ya afku da misalin ƙarfe 10 na safe a jiya Juma’a.
Shaidun gani da ido sun ce haɗarin ya afku ne bayan da kan wata gingimari ya ƙwace ya haye kan wata motar haya, inda mutane biyar su ka rasu nan take, ɗaya kuma ya ƙarasa a asibiti.
Shaidun sun ce mutum uku tsallake rijiya da baya, inda basu ji ko rauni ba a haɗarin.
Ogar Ochi, Kwamandan Hukumar Kare Tituna ta Ƙasa, FRSC, ya tabbatar da hadarin, inda ya alaƙa ta shi da gudun wuce sa’a.
Ya ce mutane 18 ne abin ya rutsa da su, inda 6 su ka mutu, tara su ka ji raunuka sannan uku su ka tsallake.