Akalla mutane shida ne suka mutu a Borno, lokacin da wata motar sufuri ta bi ta kan wata boyayyiyar nakiya da ‘yan ta’addar Boko Haram suka binne.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar karkara da ke tsakanin Bama zuwa Kawuri a karamar hukumar Konduga, inda jama’a suka saba tafiya zuwa wasu sassan jihar.
Mota kirar Toyota starlet da ta dawo daga jihar Adamawa ta taka bam din, inda ta kashe fasinjoji biyar da ke cikin jirgin.
Direban da ya samu munanan raunuka, ya mutu bayan sa’a guda a wani asibiti a Maiduguri.
Hanyar da ke tsakanin garin Bama zuwa Konduga ta kasance cikin kwanciyar hankali da lumana domin ba a samu wani hari ba a cikin shekaru 6 da suka gabata sai da maharan suka yanke shawarar tayar da bama-bamai a kan titin.
Mazauna Maiduguri sun ce sun yi mamakin yadda al’amura ke faruwa a baya-bayan nan, ganin yadda ayyukan ta’addanci ke kara zama sabon salo duk da kiran da gwamnati ta yi na mika wuya.
Idan dai za a iya tunawa gwamnati ta ce sama da ‘yan ta’adda dubu dari tare da iyalansu ne suka mika wuya duk da haka adadin hare-haren na baya-bayan nan na nuni da cewa akwai bukatar a yi da gaske dangane da ayyukan ta’addanci musamman a jihar Borno.