Bayanai na nuni da cewa, a akalla mutane 55 ne suka mutu, sakamakon fashewar wani abu a wata mahaƙar Zinariya a ƙasar Burkina Faso.
Ma’aikatan asibitin da jami’an yankin sun ce, wata guguwa mai karfin gaske ce, ta fara tashi a wurin da ke Gomgombiro a Kudu maso Yammacin kasar.
BBC ta rawaito cewa, karin mutane 50 sun jikkata, ciki har da mata da kananan yara.
Hukumomin gundumar Poni da fashewar ta afku sun kaddamar da bincike.
A na yawan samun hadari irin wannan a wuraren hakar ma’adinai na bayan fage a wasu kasashen Afirka.