fidelitybank

Mutane 52 ne suka mutu a harin Filato

Date:

Waɗanda suka rasu a harin da wasu mahara suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos na jihar Filato da ke Najeriya sun ƙaru zuwa 52, kamar yadda ƙungiyar ci gaban al’adun Bokkos ta bayyana.

Shugaban ƙungiyar, Farmasum Fuddang ne ya bayyana wa tashar Channels haka, inda ya ce an binne mutum 31 a rami ɗaya a ranar Alhamis, sannan akwai wasu guda biyar da suka ƙone a ƙauyen Hurti, sai kuma wasu guda 11 a ƙauyen Ruwi, da wasu guda huɗu a ƙauyen Manguna, da kuma wani mutum a ƙauyen Daffo.

A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Filato ta yi kira ga ƴan jihar su kwantar da hankalinsu a daidai lokacin da ake cigaba da neman waɗanda ba a gani ba.

Kwamishinar watsa labarai ta jihar, Joyce Remnap ta ce an tura jami’an tsaro yankunan domin tabbatar da zaman lafiya ya wanzu.

“Sannan an kama wasu waɗanda ake zargi suna da hannu a kashe-kashen,” in ji ta, sannan ta ƙara da cewa, “muna kira da a guji ɗaukar doka a hannu.”

Tun a farkon harin ne dai ƙungiyar makiyaya ta Gan Allah ta fito ta ce maharan ba fulani ba ne, kuma ba su da wata alaƙa da su.

tribune newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp