fidelitybank

Mutane 51 sun mutu a wata fashewa a wurin haƙar ma’adinai a Iran

Date:

Fashewar tukunyar iskar gas a wurin haƙar ma’adinai a gabashin Iran ta kashe mutane aƙalla 51, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta bayyana a ranar Lahadi.

Fiye da wasu 20 ne kuma suka jikkata bayan fashewar a lardin Khorasan ta Kudu.

An ruwaito cewa fashewar ta sinadarin methane ta afku a wasu sassa biyu na wurin haƙar ma’adinan a garin Tabas mai tazarar kilomita 540 a kudu maso gabashin Tehran, babban birnin ƙasar.

Fashewar ta afku ne da misalin karfe 9:00 agogon ƙasar a ranar Asabar, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka bayyana.

Gwamnan Kudancin Khorasan, Javad Ghenaatzadeh ya ce akwai ma’aikata 69 a wurin lokacin da aka samu fashewar.

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce: “An samu fashewar wani abu kuma abin takaici mutum 69 ne ke aiki a wurin haƙar ma’adinan a Madanjoo.

“Akwai mutane 22 a sashe na farko na wurin, sannan mutum 47 a ɗaya sassan.”

Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka rage a raye ba da kuma waɗanda suka maƙale a wurin haƙar.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp